Kalibof Ya Mayarwa Shugaban Kasar Amurka Martani Kan Mummunan Kalamansa

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayya shugaban kasar Amurka Donal Trump a matsayin mutum wanda baya iya yin magana guda ya

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayya shugaban kasar Amurka Donal Trump a matsayin mutum wanda baya iya yin magana guda ya tsaya kanta, mutumtum ne wanda yake tupka da warwara a lokaci guda.

Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto kakakin  majalisar dokokin yana fadar haka a zaman majalisar dokokin kasar a jiya Talata.

Qalibof ya kara da da cewa kalaman da Trump yake fada na kaskanta shugabannin JMI yana daga cikin yakin kwakwale ne da mutanen kasar Iran. Kuma yakamata ya sani, kuma wadanda suke tare da shi su sani mutanen Iran zasu ci gaba da kare kansu su kuma yaki da wadanda suke shishigi a kan kasarsu.

Daga karshen yan siyasan makiya ne zasu bace a cikin kwandon sharer siyasa nan ba da daewa ba.

Tun lokacinda Amurka ta kai hare-haren kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran guda uku wato Natanz ta Fordo da kuma Esfahan ne kasashen biyu suke mu sayar magangannu a tsakaninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted