Sojojin Amurka Sun Harba Tear Gas Da Albarusan Ruba Kan Masu Zanga-Zanga A Los Angeles a jiya Lahadi

Jami’an tsaro a kasar Amurka sun cilla tear gas da albarusan roba kan masu zanga-zangar kin amincewa da shirin shugaba Trump na korar wasu Amurkawa

Jami’an tsaro a kasar Amurka sun cilla tear gas da albarusan roba kan masu zanga-zangar kin amincewa da shirin shugaba Trump na korar wasu Amurkawa wadanda ya kira bakin haure.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa, rikicin wanda aka fara tun kwanaki uku da suka gabata ya tashi ne bayan da jami’an shege da fice na Amurka suka kama wasu yan Latino da nufin korarsu daga kasar. Sun kama mutane da dama a birnin Los Angeles a cikin rana kowa na gani. Gwamnan jihar Calfonia Gavin Newson ya rubuta a shafinsa na X kan cewa basu da wata matsa sai bayan da shugaba Trump ya aiko da ‘Sojojin Tarayya ko “National guard”, kuma wannan keta hurumin jihar ne, kuma shiga Trump tare da National Gurd shi ne rikita al-amura a jihar. Amma duk da haka zuwa safiyar yau Litinin kome ya lafa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted