Gwamnatin Kasar Chadi Ta Maida Martani Kan Dokar Hana Yan Kasar Shiga Amurka

Shugaban kasar Chadi Muhammad Deby ya maida martani ga shugaban kasar Amurka kan hana yan kasar Chadi shiga kasar Amurka da hana a bawa Amurkawa

Shugaban kasar Chadi Muhammad Deby ya maida martani ga shugaban kasar Amurka kan hana yan kasar Chadi shiga kasar Amurka da hana a bawa Amurkawa visar shiga kasar.

Jaridar PREMIUM TIMES  ta Najeriya ta  bayyana cewa shugaban kasar Amurka a ranar Laraban da ta gaba ne ya sanya hannu a kan dokoki wadanda suka hana yan kasashe 12 shiga kasar Amurka sannan wasu 7 kuma za’a basu Visa shigar kasar tare da sharudda.

A jiya Alhamis ne shugaban Deby ya maida martani, da haka Amurkawa shiga kasarsa. Dokar dai ta hana kasashen Afirka guda 6 shiga kasar Amurka kuma sun hada da Chadin da kuma Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia da kuma Sudan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted