Sheikh Naim Qassem Da Aragchi Sun Tabbatar Da Kara Karfin Zumunci Tsakanin Iran Da Lebanon

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Nain Qasim da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi sun gana a birnin Beirut babban birnin

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Nain Qasim da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi sun gana a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran siyasa da yankin kudancin Asiya tare da kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto aragchi yana cewa dangantaka tsakanin Iran da kungiyar Hizbullah dangane ce wacce ta shafi yankin kudancin Asiya gaba daya.

A nashi bangaren shugaban kungiyar Hizbullah sheikh Naem Kassem ya godewa JMI ta irin tallafin da take bayarwa ga kungiyoyi da kasashen kawancen masu gwagwarmaya a yankin wadanda suka hada da Falasdinawa da Lebanon da sauransu.

Aragchi ya kara da cewa Iran a shirye take ta taimakawa kasar Lebanon a harkokin siyasa tattalin arziki da zamantakewa. Ya kuma yabawa kungiyar Hizbullah kan rawan da take takawa wajen tabbatar da tsaro da kuam zaman lafiya a kasar Lebanon, musamman da HKI wacce take mamaye da wasu yankunan na kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted