Iran: Babban Kwamandan Sojojin Ruwa Na JMI Yace Sojojinsa A Shirye Suke Su Shiga Yaki Da Makiya

Babban hafsan hafsoshin sojojin JMI ya bayyana cewa sojojin kasar musamman sojojin ruwa a shirye suke su shigaba yaki dank are kasar a ko yauce,

Babban hafsan hafsoshin sojojin JMI ya bayyana cewa sojojin kasar musamman sojojin ruwa a shirye suke su shigaba yaki dank are kasar a ko yauce, ya kuma kara da cewa idan makiya sun yi wani kuskure zasu yi nadamar hakan.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Manjo Janar Mohammad Hussain Bakiri yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda shi da wasu manya manayan jami’an sojojin kasar suka kai ziyarar ganewa kansu irin shirin da sojojin kasar suke ciki a tashoshin jiragen ruwa da suke gabar tekun Farisa da kuma arewacin mashigar ruwa ta Hurmus

Tare da manjo janar Bakiri dai akwai kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC  Manjo Janar Abdolrahim Mousavi, sai kuma Manjo Janar Hossein Salami shugaban Lundunonin IRGC da kuma wasu manya-manyan jami’an sojojin kasar.

A wani labarin kuma Janar Salami babban kwamandan sojojin IRGC gaba daya ya bayyana cewa Iran zata kai hari a kan duk wani wurin da makami ya rashi zuwa kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted