Dubban Falasdinawa Sun Kauracewa Gidajensu A Dai-Dai Lokacinta Sojojin HKI Suke Fafatawa Da Dakarun Falasdinawa

Dubban Falasdinawa ne suka kauracewa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Tun ranar 21 ga watan Jeneru na wannan shekara ta 2025, wato kwanaki

Dubban Falasdinawa ne suka kauracewa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Tun ranar 21 ga watan Jeneru na wannan shekara ta 2025, wato kwanaki biyu kacal da tsaida wuta a Gaza, sojojin HKI suka fadawa sansanin yan gudun hijira na Jenen inda suka fara fafatawa da dakarun Falasdinawa a yankin. Da nufin korarsu.  

Dagan nan ne dubban Falasdinawa suka fara kauracewa gidajensu a yankin. Wasu suka dauki dukkan iyalansu su a mota su tafi inda ba’a tashin hankali. Wasu kuma sukan taka da kafafuwansu zuwa nesa daga inda ake fada da tashin hankali.

Wani dan agaji a yankin ya bayyana wa Jaridar ‘Arabsnews’ cewa bai taba ganin irin wannan kaurar da Falasdinawa suke yi ba, sai wanda aka yi a yakin 1967 inda falasdinawa 300,000 suka kauracewa gidajensu, sai kuma kafin haka a shekara ta 1948 falasdinawa 700,000 ne, sojojin yahudawan suka tilastawa falasdinawa kauracewa yankunansu a kasarsu da aka mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted