Kasar Iran Ta Yi Kakkausar Suka Kan Sabbin Takunkumin Da Amurka Ta Kakabawa Kasarta

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran ya sabawa ka’idojin dokokin kasa da kasa Kakakin ma’aikatar harkokin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran ya sabawa ka’idojin dokokin kasa da kasa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa sun sabawa ka’idojin dokokin kasa da kasa.

Baqa’i ya yi nuni da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kakaba takunkumi kan wasu kungiyoyi da cibiyoyi masu gudanar da ayyuka na dabi’a da al’adu na kasa Iran bisa zarginsu da hannu wajen sayar da danyen man fetur na Iran, a matsayin mummunan matakin da bai dace ba, kuma ya jaddada cewa hakan ya sabawa ka’idojin kasa da kasa.

Ya kara da cewa: Matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na matsin lamba ga al’ummar Iran ta hanyar hana kasuwanci da abokan huldarta na tattalin arziki shima haramtacciyar hanyar ka’idojin kasa da kasa ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted