Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Tare Da Jikkata Wasu A Kudu Maso Gabashin Kasar

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun sanar da kashe ‘yan ta’adda tare da kama wasu fiye da 50 a shiyar kudu maso

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun sanar da kashe ‘yan ta’adda tare da kama wasu fiye da 50 a shiyar kudu maso gabashin Iran

Mataimakin kwamandan shelkwatar dakarun Qudus da ke karkashin Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ahmad Shafa’i a zantawarsa da gidan talabijin na kasar a yau Asabar ya sanar da kashe wasu gungun ‘yan ta’adda tare da kame wasu 76 a lokacin wani samame mai taken “Shahidan Tsaro” da ake aiwatar a lardin Sistan da Baluchestan dake kudu maso gabashin kasar Iran.

Birgediya Janar Ahmed Shafa’i ya bayyana cewa sun fara gudanar da samamen ne tun ranar Asabar din makon jiya, inda ya jaddada cewa: Tun bayan kaddamar da shirin a ranar 27 ga watan Oktoba, ya zuwa yanzu an kashe ‘yan ta’adda 26 tare da kama wasu fiye da 50 na daban, baya ga wasu ‘yan ta’addan da suka mika wuya 12 ga jami’an tsaro.

Mai magana da yawun dakarun da suka gudanar da samamen na “Shahidan Tsaro” ya jaddada cewa: Ana gudanar da ayyukan samamen ne da hadin gwiwar al’ummar yankunan da ake gudanar da ayyukan samamen da nufin tsarkake su daga ‘yan ta’adda da kuma tabbatar da tsaro a yankunan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments