Dubun dubatar al’ummar Yemen ne suka gudanar da zanga-zangar la’antar yakin kisan kiyashi a Gaza da Lebanon
Dubun dubatar al’ummar kasar Yemen ne suka gudanar da zanga-zanga a a lardunan kasar 14 a jiya Juma’a, inda suka yi tir da yakin kisan kare dangi da haramtacciyar kasar Isra’ila take kaddamar wa a Zirin Gaza da kuma kasar Lebanon.
Dubbannin daruruwan al’ummar Yemen ne suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Sana’a karkashin taken “Muna Tare da Gaza da Lebanon… Jinin shahidai Yana Zuwa Har Zuwa Nasara.”
Zanga-zangar da jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Sayyid Abdul-Malik al-Houthi ya kira, an shirya ta ce a dandalin Al-Sab’een, filin wasa mafi girma a birnin Sana’a fadar mulkin kasar.
Masu zanga-zangar sun daga tutocin Falasdinawa, Yemen da Lebanon da kuma tutoci na yin tir da yakin kisan kiyashin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke gudanarwa a Gaza da Lebanon.