Gwamnatin ta Australiya ta hana Ayelet Shaked shiga cikin kasar domin halartar taron wata kungiya ta yahudawa.
Ita dai Shaked ta rike mukamin ministan shari’a a HKI a shekarun 2015- zuwa 2019. Sai kuma a tsakanin shekarun 2021 zuwa 2022 a matsayin ministar harkokin cikin gida.
Ita dai Ayelet Shaked tana cikin ‘yan sahayoniya masu wuce gona da iri da suke nuna adawa da kafa gwmanatin Falasdinu.
Da take mayar da martani akan matakin na kasar Austiraliya, Shaked ta zargi Canberra da cewa ta zabi zama bangaren da bai dace ba na tarihi, kuma saboda ban yarda da kafa wa Falasdinawa gwamanti ne ba aka hana ni zuwa Austiraliya.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne 21 ga watan Nuwamba ne dai kotun kasa da kasa ta manyan laifuka ta fitar da sammacin a kamo mata Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu da kuma tsohon ministansa na yaki Yoav Galalnt.