Kungiyar G20 ta yi kira da a tsagaita wuta a zirin Gaza da Lebanon a karshen taron kolin da aka gudanar a birnin Rio de Janeiro na Brazil.
Bayanin karshe na shugabannin G20 ya shiga cikin jerin batutuwa na ci gaban al’ummomi, da batun muhalli, da sake fasalin tsarin kasa da kasa.
Dangane da yakin da Isra’ila ke yi a Gaza da Lebanon, shugabannin G20 sun bayyana matukar damuwarsu game da mummunan halin jin kai da ake ciki a zirin Gaza da kuma ta’azzarar yakin Isra’ila a kan Lebanon.
Sun jaddada bukatar fadada ayyukan jin kai da kare fararen hula a yankunan da abin ya shafa.
Haka kuma, shugabannin G20 sun tabbatar da “yancin Falasdinawa na samun kasarsu mai ci gashin kanta,” tare da jaddada kudurinsu na samun sulhu da zaman lafiya ta hanyar samar da kasashe biyu Isra’ila da kasar Falasdinu da zasu zauna kafada da kafada da juna cikin lumana da aminci.
Wani sashe na bayanin bayan taro ya mayar da hankali ne kan wajabcin tsagaita bude a Gaza da Lebanon nan take, tare da wajabcin aiwatar da kudirorin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.