Falasdinawa da dama sun yi shahida yayin da wasu suka jikkata a wani kisan kiyashi da sojojin mamaya suka aiwatar a sansanin Bureij da ke tsakiyar Zirin Gaza
Kafofin watsa labaran Falasdinu sun watsa rahoton cewa: Akalla Falasdinawa 11 ne suka ne da suka hada da karamin yaro suka yi shahada sannan wasu da dama suka samu raunuka sakamakon wani harin bam da sojojin yahudawan sahayoniyya suka kai kan wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Bureij da ke tsakiyar Zirin Gaza a daren jiya Asabar wayewar garin yau Lahadi.
Shafin watsa labaran “Wafa” ya bayyana cewa: Kungiyoyin likitocin sun samu nasarar ceto gawawwakin shahidai 10 da suka hada da yara kanana da mata, baya ga wasu kimanin 20 da suka samu raunuka, inda suka garzaya da su zuwa asibiti, yayin da ake ci gaba da neman sauran wadanda suka bata.
A cikin rahotonta na kididdiga na yau da kullum, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa: A cikin sa’o’i 24, sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi kisan kiyashi a kan iyalai har sau 3, inda aka samu shahidai 35 da jikkata wasu 111 na dana da aka garzaya da su zuwa asibiti.