Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce Goyon Bayan Amurka Ne Dalilin Ci Gaba Da Yakin Gaza Da Lebanon

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Babban dalilin ci gaba da laifukan yahudawan sahayoniyya shi ne goyon bayan Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Babban dalilin ci gaba da laifukan yahudawan sahayoniyya shi ne goyon bayan Amurka

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi tsokaci kan nasarar da Donald Trump ya samu a zaben shugaban kasar Amurka, yana mai cewa; Abin da ke da muhimmanci shi ne yadda gwamnatin Amurka ke gudanar da ayyukanta a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Iran, ba wai wanda aka zaba ba.

A taron manema labarai na mako-mako da yake yi a yau litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan harin ta’addancin da aka kai a Sistan da Baluchestan, yana mai nuni da cewa irin wadannan ayyuka ba za su iya kawo cikas ga muradin mazauna kan iyakar Iran na kare kasarsu ta asali ba.

Da yake nuni da cewa jiya Lahadi 10 ga watan Nuwamba aka amince da ita a matsayin ranar kimiyya ta duniya don zaman lafiya da ci gaba, Baqa’i ya jaddada cewa yana da kyau a yi tunani a kan illar amfani da kimiyya wajen yaki.

Ya ci gaba da yin nuni da cewa, a cikin ‘yan shekarun nan, yahudawan sahayoniyya sun yi amfani da kimiyya da fasaha wajen aiwatar da shirin kisan gilla kan al’ummar Falastinu, wanda ya kasance misali a fili na laifukan yaki da kisan kare dangi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments