Ambaliyar Ruwa Ta Raba Mutane Sama Da Dubu 379 Da Muhallinsu A Kasar Sudan Ta Kudu

Ambaliyar ruwa mafi muni ta mamaye Sudan ta Kudu tare da gargadin samun ‘yan gudun hijira sama da dubu 379 Majalisar Dinkin Duniya ta sanar

Ambaliyar ruwa mafi muni ta mamaye Sudan ta Kudu tare da gargadin samun ‘yan gudun hijira sama da dubu 379

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Ambaliyar ruwa ta mamaye Sudan ta Kudu da ta shafi mutane kimanin miliyan 1.4, baya ga fiye da mutane 379,000 da suka rasa matsugunansu. Ofishin kula da jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: Ambaliyar ruwar ta shafi gundumomi 43, baya ga yankin Abyei. Kamar yadda ofishin OCHA ya yi gargadin yaduwar cutar zazzabin cizon sauro a yankunan da abin ya shafa.

Kasar Sudan ta Kudu, tana daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya, kuma ga masifar ambaliyar ruwa da take yawan fuskanta a yankunan kasar a cikin shekaru da dama musamman a arewacin kasar.

Ofishin kula da jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya watsa rahoton cewa: Ambaliyar ruwan ta shafi mazauna gundumomi 43 da kuma yankin Abyei da ake takaddama a kai tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, inda ya ce sama da mutane 397,000 ne suka rasa matsugunansu a gundumomi 22.

Ofishin na OCHA a wani rahoto da ya fitar a cikin wata daya da ya gabata ya ce kimanin mutane 893,000 ne ambaliyar ruwa ta shafa sannan sama da 241,000 suka rasa matsugunansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments