Taron Riyadh Zai Lalubo Hanyoyin Tsagaita Wutar Yaki A Gaza Da Lebanon

A Yau Litinin ne shugabannin kasashen Larabawa da na musulmi suke yin taro a binin Riyadh na Saudiyya domin tattauna hanyoyin da za a kawo

A Yau Litinin ne shugabannin kasashen Larabawa da na musulmi suke yin taro a binin Riyadh na Saudiyya domin tattauna hanyoyin da za a kawo karshen yakin Gaza da Lebanon

Daga cikin bakin da su ka fara isa birnin na Riyahd domin halartar taron da akwai shugaban  kwarya-kwayar gwamnatin Falasdinu, Muhammad Abbas.  Daga cikin wadanda ake sa ran cewa za su halarci taron da akwai mataimakin shugaban kasar Iran Muhammad  Ridha Arif, da sarkin Qatar, Tamim Bin Hamad ali-Sani.  Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta sanar da cewa Fira minister Shahbaz Sharif zai sami halarta, sai kuma shugaban kasar  Turkiya Rajab Tayyib Urdugan.

Tun a jiya ne dai kafafen watsa labarun Saudiyya su ka nuna isar shugaban kasar Nigeria Ahmad Bola Tinibu, da kuma  Najib Mikati daga kasar Lebanon.

A jiya an yi taron share fage, wanda minstan harkokin wajen Saudiyya Faisal Bin Farhan ya jagoranta, inda aka tattauna jadawalin aiki na taron na yau Litinin.

A yayin taron na jiya Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ya bukaci ganin kwamitin tsaron MDD ya fitar da kudurin da zai tilastawa HKI  kawo karshen yakin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments