Wata Sabuwar Kungiyar Ta’addanci A Arewacin Najeriya Ta Kashe Mutane Da  Kuma Sace Dabbobi A Jihar Kebbi

Sabuwar kungiyar mai suna Lakurawa ta kashe mutane 15 da kuma yin awon gaba da shanu 100 a garin Mera dake karamar hukumar Augie a

Sabuwar kungiyar mai suna Lakurawa ta kashe mutane 15 da kuma yin awon gaba da shanu 100 a garin Mera dake karamar hukumar Augie a jihar Kebbi.

Jaridar “Daily Trust” ta Najeriya ta ambato yariman Mera Alhaji Bashir Isa Mera yana tabbatar da faruwar lamarin, sannan ya kara da cewa, Lakurawan sun shiga cikin garin nasu ne a daidai lokacin da suke shirin tafiya sallar juma’a.

Har ila yau, ya kara da cewa bayan faruwar lamarin, daruruwan mutanen garin sun yi shiri su ka nufi daji domin kwato dabbobinsu.

An yi taho mu gama a tsakanin mutanen da kuma ‘yan ta’addan, da hakan ya yi sanadiyyar kashe 15 daga cikinsu da kuma Lukurawa 2.

A lokacin da ‘yan ta’addar su ka shiga garin, sun yi awon gaba ne da dabbobi, bayan da aka yi fada da su ne, su ka kashe mutane 15.

Alhaji Bashir Isa Mera ya kuma ce wadannan sabbin ‘yan ta’addar suna boyewa ne a cikin dajin Sokoto, daga can ne suke kawo hari cikin jihar Kebbi.

Watanni biyu da su ka gabata, wannan sabuwar kungiyar ta shiga garin na Mera inda ta bukaci mutane su biya zakka, sannan kuma su ka sace musu shanu. Wannan shi ne karon farko da su ka kashe mutane da kuma yin gagarumar satar shanu masu yawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments