Ofishin yada labarai na zirin Gaza, ya ce an kashe ‘yan jaridar Falasdinawa 188 tun bayan yakin kisan kare dangin da Isra’ila ta kaddamar a watan Oktoban bara.
Adadin a cewar sanarwar ya hada da wasu ‘yan jarida guda hudu da harin na Isra’ila na ritsa dasu a baya-bayan nan.
Ofishin ya ce “yana matukar yin Allah wadai da hari, da kuma kisan gillar da Isra’ila ke yi wa ‘yan jaridan Palasdinawa.
“Muna kira ga al’ummomin duniya, kungiyoyin kasa da kasa, da masu ruwa da tsaki a aikin jarida a fadin duniya da su dauki matakai a kotunan kasa da kasa domin matsin lamba wa isra’ila akan ta dakatar da kisan kiyashin da ta ke yi wa ‘yan jaridar Palasdinawa.” ” inji sanarwar.
Tun da farko dai ofishin ya ce gwamnatin Isra’ila ta yi ruwan bama-bamai wasu tantunan da ke zaman mafakar ‘yan jarida da ‘yan gudun hijira a asibitin shahidan al-Aqsa da ke birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza a karo na tara a jere.
Ta’addancin da ya lakume rayukan mutane biyu tare da jikkata wasu 26 ya zo a matsayin wani bangare na laifukan kisan kare dangi da sojojin mamaya na Isra’ila suka aikata kan asibitoci, fararen hula, da kuma ‘yan gudun hijira.
Ofishin yada labaran na falasdinu ya dora alhakin ta’asar da Isra’ilar ke aikatawa kan Amurka babbar gwamnati Tel-Aviv, da kuma sauran kasashen da ke taimakawa kisan kiyashin.