Gwamnatin Sudan ta zargin kungiyar Rapid Support Forces ta Dakarun kai daukin gaggawa da aikata kisan kiyashi a jihar Aljazira
Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta zargi dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da aikata wani sabon kisan kiyashi kan fararen hula a birnin Al-Hilalia na jihar Al-Jazira, inda aka kashe fararen hula 120 a cikin kwanaki biyun da suka gabata. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zafafa zarge-zargen cikin gida da na kasashen waje a cikin ‘yan kwanakin nan kan dakarun kai daukin gaggawa na cin zarafi da kashe-kashen jama’a a jihar Al-Jazira.
Ma’aikatar ta bayyana cewa, an kashe wadanda harin ya rutsa da su ne da harsasai, ko kuma sakamakon Sanya guba a abinci da rashin kula da daruruwan fararen hula da suka hada da maza da mata da kananan yara, wadanda dakarun kai daukin gaggawa suka yi garkuwa da su a wurare daban-daban a cikin birnin.