Mamba a Majalisar fayyace masalahar tsarin Musulunci ta kasar Iran ya fadawa Trump cewa: Manufar al’ummar Iran ita ce cimma hakkokinsu tabbatattu ba tare ganin an tauyaye musu ba
Mamba a majalisar fayyace masalahar tsarin Musulunci a kasar Iran Mohsen Reza’ei ya bayyana cewa: Aniyar al’ummar Iran ita ce neman kai wa ga hakkokinsu domin ganin sun tabbata kuma ba za su taba girgiza kan haka ba.
A cikin wani sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, Reza’ei ya kara da cewa: Dole ne Donald Trump ya yi nadamar kuskuren da ya yi a baya shi da sauran shugabannin Amurka kan munanan matakan da suka dauka kan kasar Iran.
Ya ci gaba da cewa: Manufar al’ummar Iran ita ce ganin an bi musu hakkinsu tare da tabbatar da su kuma babu abin da zai girgiza su kan kyakkyawar aniyarsu.