Kungiyar Hizbullah ta gigita gwamnatin mamayar Isra’ila ta hanyar zafafa hare-haren da take kai wa cikin kwaryar haramtacciyar kasar Isra’ila da makamai masu linzami
Ana ci gaba da samun gagarumin ci gaba a yankin kudancin Lebanon da yankin Falasdinu da aka mamaye, inda ake gwabza kazamin fada tsakanin ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila, musamman dubi da ire-iren bata-kashin da ake yi da kuma muhimman wuraren da ake kai musu hare-haren.
Rahotonni sun bayyana cewa: ‘Yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon sun kai hare-hare har sau 36 da makamai masu linzami kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila musamman kan sansanin sojojin ruwa na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin Haifa, wanda sansanin ya ƙunshi kolejin horas da manyan hafsoshin sojin ruwan yahudawan sahayoniyya, kamar yadda suka yi luguden wuta kan cibiyar rundunar soji ta Arkan da ke kudancin birnin Tel Aviv da kuma barin wuta kan yankin da ke kusa da filin jirgin sama na Ben Gurion da yankunan Kiryat Ashmona, Karyut, da kuma Safed.