Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai hare-hare a garuruwan Tel Aviv da Haifa da ke yankunan Falasdinawa da ke karkashin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da jiragen yaki marasa matuka da kuma makamai masu linzami, baya ga kaddamar da wani sabon makami mai linzami da kungiyar ta yi wanda zai shiga aiki a yakin da ake gwabzawa da yahudawan sahyuniya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya, kungiyar ta ce ta kaddamar da wani hari ta sama na daukar fansa ta hanyar harba tarin jiragen sama maras matuka a kan sansaninsojin yahudawan Isra’ila na Belo Base, wanda ke cikin rukunin runduna ta 98 na sojojin Isra’ila da ke kudancin Tel Aviv, wanda kuma shi ne karon farko da kungiyar Hizbullah ta kai hari kan wannan sansani.
Kungiyar Hizbullah ta ce ta dauki wannan matakin ne a matsayin wani bangare na jerin farmakin Khaibar a daidai lokacin da ake cika kwanaki 40 da shahadar tsohon babban sakatarebn kungiyar Sayyid Hassan Nasarallah, wanda ya yi shahada a lokacin da Isra’ila ta kai mummunan hari ta sama kan babban birnin kasar kasar Lebanon Beirut, a karshen watan Satumban 2024 da muke ciki.
Wannan ramuwar gayya, inji kungiyar, ta zo ne “domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinawa masu tsayin daka a zirin Gaza da kuma goyon bayan jajircewarsu da gwagwarmayarsu, da kuma kare Lebanon da al’ummarta.”
Kungiyar Hizbullah dai ta kai daruruwan hare-hare tun daga watan Oktoban da ya gabata, lokacin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kaddamar da yakin kisan kare dangi a kan Gaza, tare da kara zafafa hare-haren wuce gona da iri kan kasar Labanon.