An sake zaben Musulmai biyu mata ‘yan majalisar dokokin Amurka

Rashidah Tlaib, wakiliyar majalisar wakilai daga jihar Michigan da Ilhan Omar, wakiliyar Minnesota, sun sake lashe zabe majalisar dokokin Amurka. A rahoton tashar talabijin na

Rashidah Tlaib, wakiliyar majalisar wakilai daga jihar Michigan da Ilhan Omar, wakiliyar Minnesota, sun sake lashe zabe majalisar dokokin Amurka.

A rahoton tashar talabijin na Aljazeera, ‘yan majalisar Musulmi biyu, Rashida Talib da Ilhan Omar, sun sake lashe zaben majalisar dokokin Amurka. Sun kafa tarihi a lokacin da sukashiga wannan majalisa a matsayin wakilan majalisar dokokin Amurka a shekarar 2019, inda suka zama mata musulmi na farko da suka shiga wannan majalisa.

Ilhan Omar, wacce aka haifa a shekarar 1982, ‘yar siyasa ce ‘yar asalin kasar Somaliya.  An haifi Ilhan Omar a Somaliya a cikin iyali musulmi. Ta zama memba na Majalisar Wakilai ta Minnesota a cikin 2016 kuma ita ce  Ba’amurka musulma ta farko mai sanye da lullubi da ta zama memba na wannan majalisa.

A ranar 6 ga Nuwamba, 2018, ta lashe zaben Majalisar Wakilan Amurka kuma an zabe ta  matsayin ‘yar majalisar daga mazaba ta biyar ta Minnesota.

Ita ce mace ta farko da ke sanye da hijabi, mace ta farko ‘yar gudun hijira, tare da Rashida Talib, ita ce mace Musulma ta farko a Majalisar Wakilan Amurka. Ta yi hijira daga Somalia a 1990 a lokacin yakin basasa kuma ta zauna a sansanin ‘yan gudun hijira a Kenya na tsawon shekaru hudu kafin ta yi hijira zuwa Amurka.

Ita kuwa Rashida Tlaib ‘yar asalin Falastinu ce, an haife ta a shekara ta 1976, yar siyasa ce kuma lauya. Ita ‘yar jam’iyyar Democrat ce kuma tsohuwar ‘yar majalisar wakilai ta Michigan, kuma lokacin da aka zabe ta a matsayin wakiliyar majalisar wakilai ta Michigan a 2009, ita ce mace Musulma ta farko a wannan majalisa.

A shekarar 2018, jam’iyyar Democrat ta tsayar da ita takarar majalisar wakilai ta Amurka da kuma zama a mazabar Michigan ta 13, kuma a babban zaben kasar, tare da Ilhan Omar, sun zama na farko.

Ita ce mace ta farko da ta fara shiga wannan majalisa ‘yar asalin Falasdinu, sannan kuma ta taka rawar gani wajen nuna adawa da matakin da gwamnatin Amurka take dauka wajen mara baya ido rufe ga laifukan yakin Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments