Iran ta ce sakamakon zaben shugaban kasar Amurka da ya nuna Donald Trump na kan hanyarsa ta zuwa fadar White House ba wani batu ba ne a gare ta, duk da cewa zai iya sanyawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran karin takunkumi.
A shekarar 2018 ne Amurka, karkashin Shugaba Trump, ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla a shekarar 2015 da Iran, sannan ta kakaba wa Jamhuriyar Musulunci takunkumai masu tsauri.
Da take mayar da martani kan yiwuwar samun nasarar Trump a zaben, mai magana da yawun gwamnatin Fatemeh Mohajerani ta shaidawa manema labarai cewa a wajen Iran ba wani bambanci tsakanin Trump da abokiyar hamayyarsa Kamala Harris a zaben.
Mohajerani ta ce, an riga an yi dukkan shirye-shiryen da suka dace,” kuma Iran a shirye take ta tunkari duk wani sabon takunkumi.
Tsawon shekaru arba’in na takunkuman da aka kakabawa Iran, sun sanya kasar ta samu ci gaba a fanonni da dama.