Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasar Amurka, inda ya kayar da Kamala Harris.
Nasarar da Trump ya samu ta zo ne a bayan yakin neman zabe mafi muni da ak samu a tarihin Amurka.
“Nasarar siyasa ce da kasarmu ba ta taba ganin irinsa ba,” kamar yadda Trump ya shaidawa magoya bayansa a Florida.
Trump ne kadai aka zaba a matsayin wanda aka samu da laifi. A ranar 26 ga watan Nuwamba zai fuskanci hukunci a gaban wata kotu a birnin New York bisa laifin zamba.
Trump mai shekaru 78 da haihuwa, yana kan hanyarsa ta shiga tarihin shugabannin Amurka mafi dadewa kan mulki.
Zai zarce Joe Biden wanda zai yi murabus a watan Janairu yana da shekaru 82.
Nasarar da Trump ya samu, biyo bayan yakin neman zabe mai cike da rudani, na da tasiri a gida da waje.
Barazanar da ya yi na korar bakin haure ba bisa ka’ida ba ya tayar da hankali matuka a yankin Latin Amurka.
Matsayinsa na “Amurka da Farko” yana da matukar damuwa ga Turai da NATO.
Da take mayar da martani kan sakamakon, kakakin gwamnatin Faransa ta ce dole ne Turai ta amince da daukar nauyin al’amuranta.
Trump dai na da sabani da kasashen turai da dama game da yakin Ukraine.