Babban jami’i a kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, Sami Abu Zuhri, ya yi tsokaci kan korar ministan tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila Yoav Gallant da fira ministan mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi a yammacin ranar Talata.
Abu Zuhri ya ce Netanyahu ya kori Gallant, wanda ke takama da cewa zai kawo karshen kungiyar Hamas.
Abu Zuhri ya kara da cewa: “A yau suna fadawa mutane cewa: Gallant ya tafi, amma Hamas tana nan daram, kuma za ta ci gaba da gudanar da gwagwarmaya da Yardan Allah Madaukaki.
A yammacin jiya ne gidan rediyon yahudawan sahayoniyya ya sanar da cewa: Netanyahu ya kori Gallant daga ma’aikatar yaki tare da nada Israel Katz a madadinsa, yayin da Gideon Saar ya zama ministan harkokin waje.
Mamban Majalisar Dokokin Isra’ila ta Knesset Tali Gotlev ya ce: Korar Gallant ta zo a makare, amma ya fi a cewa yana nan a cikin gwamnatin kasar, saboda ya yi illa ga tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila. A nata bangaren, Kungiyar iyalan gidan yahudawan da ake tsare da ‘yan uwansu a Gaza, sun bayyana cewa korar Gallant ci gaba ne na kokarin da Netanyahu na kin gudanar da yarjejeniyar sakin ‘yan uwansu da suke hannun ‘yan gwagwarmaya a matsayin fursunoni a Gaza.