Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya kan Falasdinu, Francesca Albanese, ta jaddada cewa: Abin da ke faruwa a Gaza dangane da matsalar yunwa wani tsari ne da aka shirya da nufin halaka al’ummar Falasdinu ba yaki ba ne, sai dai a kira shi “kisan kare dangi”.
Albanese ta bayyana a shafinta na dandalin X a rahoton da ta aikewa Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa a watan da ya gabata, cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kyale manyan motocin agaji 30 kacal a kowace rana su shiga yankin Zirin Gaza.
Albanese ta jaddada cewa: Akwai hanyoyi da dama da haramtacciyar kasar Isra’ila take amfani da su wajen rusa rayuwar Falasdinawa, inda ta yi nuni da cewa mafi zalunci da sarkakiya a cikin su shi ne haifar da rashin dorewar rayuwa da rashin dan Adamtaka.
Albanese ta jaddada cewa: Kada a kira abin da ke faruwa a Falasdinu da yaki, saboda kisan kare dangi ne ake aiwatarwa a fili, kuma manufar halaka Falasdinawa ta bayyana a fili, kamar yadda da hadin gwiwar wasu kasashe ake tafka wadannan munanan ayyuka.
A ranar litinin da ta gabata ce, babban kwamishinan hukumar bada agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta rage yawan motocin da suke jigilar kayayyakin ba da agajin da aka ba su izinin shiga Zirin Gaza zuwa manyan motoci 30 kacal a kowace rana a cikin watan Oktoban da ya gabata.