Mutane 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani farmaki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan garin Barja da ke kudancin Beirut na kasar Lebanon
Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa: Akalla mutane 20 ne suka mutu yayin da wasu 14 na daban suka jikkata sakamakon wani farmaki da jirgin saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya kai kan wani gini a garin Barja da ke gabar teku, wanda ke da nisan sama da kilomita 20 kudancin birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon.
Ma’aikatar lafiyar ta ce: Ana ci gaba da aikin ceto ko akwai wasu mutane a karkashin baraguzan gininda ya rufta sakamakon harin. A baya dai ma’aikatar ta bayyana cewa harin da aka kai a Burja ya yi sanadiyar mutuwar mutane 15 ne tare da jikkata wasu, kafin ta sanar da cewa adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 20.
Hayaki ya ci gaba da tashi daga ginin a yammacin jiya Talata, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, yayin da iyalai da dama suka tsere daga yankin.