A wata gaggarumar zanga-zangar ba zato ba tsammani da ta barke bayan korar ministan tsaron Haramtacciyar Kasar Isra’ila Yoav Gallant da Benjamin Netanyahu ya yi, dubban yahudawa masu zanga-zanga sun toshe babbar hanyar Tel Aviv – Ayalon, lamarin day a kawo babban tsaiko da cunkoso na ababen hawa.
Zanga-zangar ta barke ne a daren jiya Talata, inda masu zanga-zangar suka fara kona tayoyi a kan tituna da saka shingaye na wucin gadi a kan tituna.
Gaggawa da rashin shiri na zanga-zangar ya sa ‘yan sanda ba su iya shawo kan lamarin ba, domin kuwa sun kasa hana masu zanga-zangar rufe hanyoyi da kafa shingaye a kan tituna.
Bayan korar tasa, Gallant ya yi wata sanarwa, inda ya bayyana cewa sabanin ikirarin Netanyahu, korar tasa ta shafi matsayarsa ne kan daftarin dokar tsattsauran ra’ayi da Netanyahu ke yunkurin zartarwa.
Ya kuma soki yadda Netanyahu ke fuskantar yakin da yake yi yana mai cewa “Mun rasa daruruwan mayaka da sojoji a wannan yakin, kuma muna dauke da nauyin dubban wadanda suka jikkata da nakasassu, kuma har yanzu ana ci gaba da yakin.”
Gallant ya yi gargaɗi game da manyan ƙalubalen da ke gaban Isra’ila, yana mai cewa, “Shekaru masu zuwa suna tafe da matsaloli masu yawa da kalubale mai wahala; kuma yake-yake ba su kare ba.