An Fara Kamen ’Yan Najeriya A Libya Biyo Bayan Hukuncin CAF

’Yan Najeriya mazauna kasar Libya, sun shiga firgici bayan da Hukumomi suka fara kamen su biyo bayan hukuncin da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF)

’Yan Najeriya mazauna kasar Libya, sun shiga firgici bayan da Hukumomi suka fara kamen su biyo bayan hukuncin da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta yanke.

Lamarin ya faru ne bayan ƙorafin da Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), ta shigar kan yadda aka wulakanta ’yan wasan tawagar Super Eagles a kasar Libya a kwanakin baya.

Wata majiya a kasar ta ce: “Sun riga sun fara kamen. Labarin ya zo min cewar sun fara kamen a ranar Asabar, sun ce ba za su biya tarar ba.”

Tawagar Super Eagles ta fuskanci ƙalubale a kasar inda suka shafe sama da sa’o’i 18, ba tare da samun wajen kwana ko abinci ba.

Tawagar ta je Libya ne domin buga zagaye na biyu na wasan neman gurbin Gasar Kofin Afrika, biyo bayan nasarar da suka yi da ci daya mai ban haushi a birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom.

Hakan ne ya sa, CAF ta soke wasan, tare da bai wa Najeriya kwallaye uku da maki uku, tare da cin tarar Libya dala 50,000.

Wannan hukunci ta sanya kafafen yaɗa labarai na Libya, bukatar a kama ’yan Najeriya danke zaune a kasar ba bisa ka’ida ba.

Sun bayyana cewar kudin da aka ci tarar kasar kamata ya yi a samo su a wajen ’yan Najeriya ta hanyar kame.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments