Kungiyar Hizbullah Ta Kai Hare-Hare Kan Sansanin Leken Asirin ‘Yan Sahayoniyya A Wajen Birnin Tel Aviv

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai hare-haren bama-bamai kan sansanin leken asirin sojin Isra’ila da ke wajen birnin Tel Aviv Mayakan

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta kai hare-haren bama-bamai kan sansanin leken asirin sojin Isra’ila da ke wajen birnin Tel Aviv

Mayakan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon sun kai jerin hare-hare kan sansanin Glilot na rundunar leken asirin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila mai lamba 8200 da ke wajen birnin Tel Aviv da wasu makamai masu linzami.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, ta kai wasu hare-haren makamai masu linzami a safiyar yau Laraba kan rundunar leken asirin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila mai lamba 8200.

Har ila yau, kafafen watsa labarai na yahudawan sahayoniyya sun tabbatar da jin karar fashe-fashen wasu abubuwa a birnin Tel Aviv da kuma dakatar da zirga-zirga a filin jirgin sama na Ben Gurion.

Har ila yau, cibiyar motocin daukar marasa lafiya ta yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya ta sanar da cewa ta samu rahoton jikkata yahudawan sahayoniyya sakamakon turmutsitsin da suke wajen neman shiga maboyar karkashin kasa bayan harba rokoki daga kasar Lebanon kan birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments