Sojojin Yemen Sun Kai Hari Kan Sansanin ‘Yan Sahayoniyya Da Makami Mai Linzami

Sojojin kasar Yemen sun kai hari kan wani sansanin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Sojojin Yemen sun sanar da kai wani

Sojojin kasar Yemen sun kai hari kan wani sansanin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami

Sojojin Yemen sun sanar da kai wani gagarumin farmakin soji kan wani sansanin sojin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke gabashin yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami kirar Falasdinu 2.

A sanarwar da rundunar Sojin kasar ta Yemen ta fitar ta sanarwar cewa: Makami mai linzami da ta harba ya yi nasarar kai wa, inda aka saita shi, inda ya ketare tsarin shige tsaron Amurka da na yahudawan sahayoniyya.

Sojojin Yemen sun jaddada cewa: Za su ci gaba da kai farmakin soji kan makiya yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida har sai an daina kai hare-haren wuce gona da iri kan Falasdinawa tare da janyewar sojojin mamaya daga yankin Zirin Gaza gami da kawo karshen farmaki kan kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments