Hamas ta ce Arewacin yankin Gaza na fuskantar manyan laifuffukan da suka kai na kisan kiyashi, da suka hada da kisa a fili, kashe fararen hula da gangan, kame, da kuma tilasta mutane yin gudun hijira da Isra’ila ke yi, kamar yadda babban kusa a kungiyar Hamas, Osama Hamdan ya sanar a wanann Talata.
A wani taron manema labarai da ya kira, Hamdan ya ce wannan ta’asa na zuwa ne a daidai lokacin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke kara tsananta hare-hare da kuma jefa al’ummar Gaza a cikin yunwa, da killace su, gami da kai hare-hare a kan asibitoci, da rusa gidaje, da kuma hana shigar da kayan agaji da makamashi.
A rana ta 18 a jere, Isra’ila na ci gaba da tsananta killace arewacin Gaza, musamman ma a Jabalia da Beit Lahia, da nufin tarwatsa al’ummar Palastinu. in ji Hamdan.
Ya ce “Isra’ila” ta yi watsi da dukkan kiraye-kirayen da kasashen duniya suka yi na ba da damar shigar da mai a asibitoci, da abinci, da magunguna, da kuma bukatar ceto wadanda suka makale a karkashin baraguzan gine-gine.
Ya kara da cewa gawawwakin shahidai da wadanda suka jikkata suna kan tituna, yayin da ake harbin motocin daukar marasa lafiya don hana su isa gare su.
Hamdan ya yi nuni da cewa, hakan ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan majiyyata da kuma jikkata wasu, lamarin da ya haifar da munanan yanayi da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ke barazana ga rayuwar dubban mutane .