Mataimakin Shugaban Kasar Kenya Da Aka Kora Ya Ce Rayuwarsa Tana Cikin Hatsari

Mataimakin shugaban kasar Kenya da aka kora na fargabar tsaron lafiyarsa bayan an janye jami’an tsaronsa Hambararren mataimakin shugaban kasar Kenya, Rigathi Gachagwa, ya tabbatar

Mataimakin shugaban kasar Kenya da aka kora na fargabar tsaron lafiyarsa bayan an janye jami’an tsaronsa

Hambararren mataimakin shugaban kasar Kenya, Rigathi Gachagwa, ya tabbatar a ranar Lahadin da ta gabata cewa: Hukumomin Kenya sun janye tawagar jami’an tsaro da take kare lafiyar tsohon mataimakin shugaban kasar Kenya, tare da dora wa shugaban kasar William Ruto alhakin kare lafiyarsa, jim kadan bayan da majalisar dattawan kasar ta kada kuri’ar tsige shi daga mukaminsa bayan da aka zarge shi da keta kundin tsarin mulkin kasar da tunzura kiyayyar kabilanci.

Gachagwa, wanda ya musanta tuhumar da ake masa da bayyana tuhumar a matsayin makircin siyasa, ya shaidawa manema labarai cewa tsaron lafiyarsa na cikin hadari. Ya kara da cewa, “Abu mafi muni da ya taba faruwa a kasarsa shi ne mutum ne wanda ya taimaka maka ka zama shugaban kasa, yana nufin Ruto, wanda ya goyi bayan takararsa a zaben 2022 amma aka shirya makarkashiyar yin fatali da shi daga fagen siyasa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Risila Onyango ta ki cewa uffan kan furucin tsohon mataimakin shugaban kasar. Sannan kakakin Ruto ya ce za su yi tsokaci daga baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments