Hezbollah ta harba manyan makamai masu linzami a kan Haifa

Kungiyar Hezbollah ta kaddamar da wasu jerin hare-haren makami mai linzami fiye da 200 a cikin kasa da sa’oi 24 da suka gabata a kan

Kungiyar Hezbollah ta kaddamar da wasu jerin hare-haren makami mai linzami fiye da 200 a cikin kasa da sa’oi 24 da suka gabata a kan birnin Haifa da wasu yankunan arewacin Falastinu da yahudawa suka mamaye.

Bugu da kari, mayakan Hizbullah a bangaren tsaron sararin samaniya sun yi  ruwan wuta a kan wani jirgin yaki marasa matuki day a shiga cikin yankunan kudancin Lebanon.

Hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yin arangama mai tsanani tsakanin dakarun na Hizbullah da kuma sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila da ke son yin kutse a yankunan kudancin Lebanon.

Kungiyar Hizbullah ta tsananta kai hare-hare kan sansanonin sojin Isra’ila a matsayin martani ga hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Labanon da Gaza.

Mayakan kungiyar Hizbullah sun kai hari a wasu dandazon sojojin yahudawa da suka kutsa kai a yankin Wadi Hounin da ke yammacin garin Odaisseh na kasar Labanon, inda suka yi amfani da makaman roka masu yawa wajen kai.

Jim kadan kafin hakan, mayakan na Hizbullah  sun harba makamin roka a sansanin sojin Filon da ke Rosh Pina, a gabashin birnin Safad da ke arewacin Falastinu da yahudawa suka mamaye.

Kungiyar Hizbullah dai ta ci gaba da kai hare-hare a duk tsawon wannan ranar jiya babu kakkautawa, inda rahotanni suka tabbatar da cewa jiragen Isra’ila masu saukar angula sun yi ta kai komoa  kan iyaka da Lebanon, domin kwasar gawawwakin sojojin yahudawa da suka halaka ko suka jikkata sakamakon hare-haren dakarun Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments