Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare Hare A Kan Bait-Lahia Na Zirin Gaza Inda Suka Kashe Falasdinawa Kimani 80

A wani sabon kisan kiyashi da jiragen yakin HKI suka kai zirin Gaza sun kashe mutane akalla 80 a garin Beit Lahiya. Kamfanin dillancin IP

A wani sabon kisan kiyashi da jiragen yakin HKI suka kai zirin Gaza sun kashe mutane akalla 80 a garin Beit Lahiya.

Kamfanin dillancin IP na kasar Iran ya nakalto shugaban asbitin Kamal Adwan yana cewa da dama daga cikin wadanda suka ji raununa sun rasa wasu gabban jikinsu, sannan wasu kuma sun yi shahada saboda zubar jinni saboda rashin kayakin aiki da kuma kwararrun likitoci a asbitin.

Hussam Abu Safiya, shugaban asbitin Kamal Adwan a Beit Lahia, ya kara da cewa, suna fama da karancin kayakin aiki da magunguna a asbitin. Ya ce a hare-haren yau Lahadi akwai wasu da dama wadanda suke karshen gine ginen da suka fada a kansu sanadiyyar karfin boma boman da jiragen saman yahudawan suka jefa a kansu.  

Kungiyar Hamas ta yi tir da hare haren na Beit-Lahiya ta kuma bayyana na su a matsayin shaida wacce take tabbatar da cewa HKI ta na son kashe mutanen gaza gaba daya ne.

A wani labarin kuma kungiyar ta Hamas ta ba da labarin kashe wani babban kwamandan sojojin HKI a Gaza mai mukamin leutanan a yammacin yau Lahadi. Ehsan Daksa da wasu sojojin a rundunasa mai lamba 401 sun halaka ne a cikin tankunan yakin guda biyu wadanda kungiyar Hamas ta tarwatsa su a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments