An Bude wa Sojojin HKI Wuta Akan Iyaka Da Kasar Jordan

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; sojoji biyu sun jikkata akan iyaka da Jordan sanadiyyar tsallako iyaka da wasu mutane uku su ka yi,

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; sojoji biyu sun jikkata akan iyaka da Jordan sanadiyyar tsallako iyaka da wasu mutane uku su ka yi, suna sanye da kayan soja.

Radiyon sojan HKI ya ambaci cewa an harbi sojojin biyu ne a kusa da tafkin “Dead Sea” da nisan kilo mita 3 daga sansanin ‘yan share wuri zauna na “ILOT”.

Tuni gwamnatin kasar Jordan ta karyata cewa wasu mutane masu sanye da kayan sojan kasar sun tsallaka iyaka.

Tashar talbijin ta aljazira ta bayar da labarin da yake cewa, an kashe biyu daga cikin maharan, yayin da na uku ya tsere, sai dai ana cigaba da nemansa.

Tashar talbijin ta 12; ta ambaci cewa; binciken da ake gudanarwa na tsaro yana nuni da cewa, mutane ukun da su ka ketaro iyaka suna sanye da kayan sojan gwamnatin Jordan.

 Tashar talabijin din sojan HKI ta kuma ce, sojoji suna cigaba da bincike da bin sawun  daya daga cikin mutanen uku da ya yi batan dabo.

Sai dai kuma wata sanarwar ta  soja ta ambaci cewa;  Sun ga wasu masu dauke da makamai da yawa sun tsallaka iykar Jordan zuwa yankin Kudancin tafkin “Dead Sea.”

An ga jiragen sama masu saukar angulu na soja suna shawagi a kusa da iyakar Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments