Makaman Hizbullah Sun  Mayar Da Birnin Haifa Kango

A cigaba da kai wa garuruwa da biranen HKI hare-hare, Hizbullah ta harba makamai masu linzami da dama a birnin Haifa wanda shi ne birni

A cigaba da kai wa garuruwa da biranen HKI hare-hare, Hizbullah ta harba makamai masu linzami da dama a birnin Haifa wanda shi ne birni na biyu bayan Tel Aviv.

Dan rahoton tashar talbijin din Aljazira daga Ramallah ya bayyana cewa; Saboda yawan hare-haren da dakarun na Hizbullah suke kai wa birnin Haifa, da dama daga cikin mazaunansa sun fara tunanin ficewa daga cikinsa.

Tun da safiyar yau Juma’a ne dai dakarun na Hizbullah suke harba makamai masu linzami samfurori mabanbanta akan garuruwan HKI da su ka hada da Haifa, Akka da yakin tuddan Gulan dake karkashin mamaya.

Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; Jiniyar gargadi ta rika kadawa a yankin tuddan Gulan sanadiyyar makamai masu linzami da aka harba daga Lebanon.

A gefe daya kafafen watsa labarun na HKI sun ambaci cewa, uku daga cikin zaratan sojojinsu na rundunar Gulani sun sami raunuka masu hatsari a yakin da ake yi a kudancin Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments