Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Tokwaransa Na Kasar Oman A Birnin Mascat

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Omman Sayyid Badar Al-busa’idi a birnin Mascat babban birnin Omman a safiyar

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Omman Sayyid Badar Al-busa’idi a birnin Mascat babban birnin Omman a safiyar yau Litinin.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran na fadar cewa ministan ya tattauna da tokwaransa na kasar Omman kan al-amura da dama daga ciki har da batun tsagaita wuta a yakin da ke faruwa da HKI a Gaza da Lebanon.

Kafin haka dai ministan ya ziyarci wasu kasashen yankin wadanda suka hada da Lebanon, Siriya, Saudiyya, Qatar da kuma Iraki da kuma ita omman.

Tare da bayyana Shirin kasar Iran na karban duk wata hanya ta tattaunawa don dawo da zaman lafiya a yankin, Aragchi ya ce kasarsa a shrye take ta shiga yaki da HKI da kuma kawayenta idan har ta kama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments