Ministan harkokin wajen Iran ya isa birnin Riyadh a wani rangadi da ya fara a yankin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiyya, a wani rangadi da ya fara a kasashen yankin gabas ta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiyya, a wani rangadi da ya fara a kasashen yankin gabas ta tsakiya.

A yammacin wannan Talata a birnin Tehran, Araghchi yayi jawabi ga manema labarai inda ya ce; “Tattaunawarmu da dukaknin banagrori tana ci gaba da gudana dangane da ci gaban da ake samu a yankin, da nufin dakile laifukan yaki da gwamnatin yahudawan Sahayoniya take aikatawa a Lebanon, da kuma kisan kare dangi a yankin zirin Gaza.”

Da yake karin haske kan matsayin Iran kan gwagwarmayar al’ummar yankin, ya ce: Manufar Iran ita ce goyan bayan gwagwarmayarsu, kuma wannan wata manufa ce ta asali mai tushe a cikin manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma ba za mu taba yin watsi da wannan manufar ba,” in ji shi.

“Shawarwarin da muke yi da sauran bangarori na da nufin ganin an dakatar da wadanann laifuka da Isra’ila take aikatawa, da dakatar duk wasu tashe-tashen hankula da samar da zaman lafiya a yankin.” In ji Araqchi.

Game da shirye-shiryen dakarun kasar Iran kuwa, ministan harkokin wajen kasar ya ce, “A shirye muke domin fuskantar kowane irin yanayi, kuma dakarunmu suna cikin babban  shirin ko ta kwana fiye da kowane lokaci.”

A ranar 4 ga watan Oktoba ne Araghchi ya bar Tehran zuwa Beirut, a wani bangare na rangadinsa a yankin, inda kuma ya tattauna da jami’an gwamnatin Lebanon, kafin daga bisani kuma ya wuce zuwa kasar Syria, inda ya gana da shugaba Bashar Assad da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments