Hudubar Jagora Ta Sallar Juma’a 05 Oktoba 2024

                  Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai. Ina yi masa godiya, ina kuma neman taimakonsa. Ina

                  Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai. Ina yi masa godiya, ina kuma neman taimakonsa. Ina neman gafararsa, ina kuma dogaro da shi. Kuma ina yin salati da sallama ga masoyinsa, manzonsa mafi girma, shugabanmu, Muhamma al-Mustafa ( s.aw.) da iyalasa tsarkaka,musaman ma dai  Ali Amirul-Muminin, da abin kaunarsa, Az-Zahra,al-mardhiyya, da Hassan da Husain, shugabannin samarin gidan aljanna,da Aliyu Bin Husain Zainul-Abidin, da Muhamamdu Bin Ali al-Bakir, da Ja’afar Bin Muhammad, As-Sadiq, da Musa Bin Ja’afar al-Kazim, da Aliyu Bin Musa al-ridha, da Muhammad Bin Ali al-Jawad, da ali Bin Muhamamd al-Hadi, da Hassan Bin Ali,al-zaki, al-Askari, da Hujjar Allah, wanda zai tsayar da adalci, al-Mahadi, tsaira da amincin Allah a gare su baki daya. Ina kuma yin gaisuwa ga sahabban –maznon Allah-zababbu, da duk wanda ya bi su cikin kyautatawa har zuwa ranar kiyama. Haka nan kuma masu kare raunana da masu jibintar muminai.

 Na zabi ace  a wurin wannan sallar juma’ar  anan Tehran ne zan girmama dan’uwana, abin kaunata, kuma abin alfaharina, mutumin da yake da tagomashi a duniyar musulunci, wanda yake da harshe mai balaga wajen Magana da mutanen wannan yankin, wanda kuma yake a matsayin lu’u lu’u mai haskawa na kasar Lebanon. Abin girmamawa  Sayyid Hassan Nasarallah Allah ya yarda da shi.  Zan kuma yi Magana akan wasu batutuwa.

Wannan hudubar ina yinta ne ga al’ummar Musulmi baki daya,amma kuma za ta kasance ta musamman ga al’ummun kasashen Lebanon da Falasdinu mai girma. Mu da ku duka, mun kadu saboda shahadar Sayyid abin kauna, rashi ne mai girma wanda dukkaninmu mun kadu da dukkanin abinda wannan Kalmar take nufi. Sai dai kuma alhinin da muke yi, baya nufin gwiwarmu za ta yi sanyi ko mu yanke kauna da fadawa cikin zullumi. Alhimin da muke yi, yayi kama da irin wanda muke yi wa shugaban Shahidai Husain Bin Ali amincin Allah ya tabbata a gare shi, wanda yake jaddada rayuwa, yake bayar da darussa,da karfada azama da cusa fata.

 Sayyid  Hasan Nasrallah ya rabu da gangar jikinsa, amma shaksiyyarsa ta hakika da ruhinsa da gwabensa, da sautinsa mai karfi, za su gaba da wanzuwa a cikinmu.

Hakika, shi ya kasance wanda ya daga tutar fada da shaidanu da ja’irai masu wawason albarkatun kasashe. Ya kuma kasance ma’abocin balaga a harshensa na kare wadanda aka zalunta, mai kare su cikin jarunta. Har ila yau ya kansace mai goyon bayan dukkanin masu gwagwarmaya akan tafarkin gaskiya, kuma mai karfafa su. Kwarjininsa da tasirinsa sun tsallake iyakokin Lebanon da Iran da kasashen Larabawa, kuma shahadarsa a wannan lokacin za ta kara zurfin tasirinsa.

Mafi muhimmancin sakwanninsa na zance da aiki a cikin rayuwarsa ta duniya a gare ku, ya ku al’ummar Lebanon, su ne; Kar ku zama masu yanke kauna, kar ku girgiza saboda gushewar fitaccen mutum kamar yadda ta kasance da Imam Musa As-sadar, da sayyid Abbas Musawi. Kar ku bari shakku ya shige ku dangane da godaben da kuke tafiya akansa na gwagwarmayarku. Kum rubanya kwazonku da kuma karfin da kuke da shi, ku kuma karfada hadin kanku. Ku yi gwagwarmaya da abokan gaba masu wuce gona da iri, kuma sa ya ci kasa ta hanyar dogaro da imaninku da kuma tawakkalinku.

 Ya ku abin kaunata!, ya al’ummar Lebanon ‘yan amana, ya samarin Hizbullah, da kungiyar Hamas, da kuke cike da qumaji! Ya ku ‘ya’yana, wannan shi ne abinda Sayyin dinmu, Shahidi yake bukata a wurinmu a wannan lokacin, shi ne kuma abinda kungiyar gwgawarmaya take bukata daga gare ku, haka nan kuma shi ne abinda dukkanin al’ummar musulmi suke bukata daga gare ku.

Abokin gaba, kamazi, matsoraci, da ya ga cewa, ya kasa rusa kungiyoyin Hizbullah, Hamas, da Jihadul-Islami, da sauran kungiyoyin gwgawarmaya, sai ya buge da yin kisan kiyashi da rusau, da kashe fararen hula.

Amma  menene sakamakon karshe?  Ba wani abu da  su ka cimmawa saboda wannan abinda su ka aikata idan ba fushi-daga al’umma ba, da kuma kara kaimin gwgawarmaya ba? Haka nan kuma bullar wasu mazaje da jagorori da masu sadaukarwa. Zai kuma kara takurawa wannan kurar mai shan jini cikin da hana ta sakat, wanda a karshe zai kai ga shafe ta daga fagen samuwa, da yardar Allah.

Ya ku abin girmakawa, zukatan da   bakin ciki yake sa mju girgiza, suna samun nutsuwa daga ambaton Allah, da kuma neman samun nasara daga gare shi. Za a iya gyara abubuwan da aka lalata, hakurinku da tsayin dakarku, zai samar da daukaka da karama.

Hakika Sayyid, ya kasance jagoran gwgawarmaya mai wuya a tsawon shekaru talatin, ya kuwa daukaka matsayin kungiyar Hizbullah mataki-mataki:

“ Kamar shuka ce da ta fitar da tsakintam,ya karfafata, su ka kuma yi kauri, su ka daidaita a kan itatuwnasu don ya ba wa manoma sha’awa,don kuma ya fusata wdanda su ka kafirta da su. Allah ya yi wa wadanda su ka ba da gaskiya su ka kuma yi ayyuka nagari daga cikinsu alakwalin gafara da kuma lada mai girma.” Surat Fathi: 29

Ta hanyar matakan da Sayyid ya rika dauka, kungiyar Hizbullah ta rika girma, sannu a hankali, ya kasance ta hanyar hakuri da aiki da hankali, sakakamon samuwarsa ta tabbata ga makiiya a cikin matakai da zango-zango mabanbanta, ta hanyar samun nasara akan ‘yan sahayoniya abokan gaba:

“ Tana bayar da ‘ya’yanta a kodayaushe,da izinin Ubangijinta.” Suratu Ibrahim: 26

Tabbas, Hizbullah ta kasance tamkar bishiya ce dai dadin ‘ya’ya,kuma Shahidin jagoranta ya kasance daya daga cikin ‘ya’ya masu nagarta da kasar Lebanon ta samar a tsawon tarinta.

Tun zamani mai nisa da tsawo, mu Iraniya mun san falalar kasar Lebanon, domin malamanta sun yi wa Iran ruwan ilimi a zamunan daulolin Sarbidari da Safawi a karnuna na  takwas, da goma da goma sha daya na hijira. Daga cikinsu da akwai Muhammad Bin Makki, al-Amuli, shahidi. Da Aliyu Bin al-Alkarki. Da Zainulabidin al-Amili, al-shahid. Da Husain Bin aldussamad, al-amuli da dansa Baha’uddini wanda aka fi sani da Sheikh Baha’i da wasu da dama daga cikin malaman addini da ilimi.

A dalilin haka, kasar Lebanon da aka yi wa illa, tana da bashi a wuyanmu da ya zama wajini mu biya shi, kuma wajibi ne a wuyayen dukkanin musulmi.  Hizbullah da kuma Sayyid Shahidi, da  su ka shiga yaki domin goyon bayan gaza, da kuma yin jihadi domin kare masallacin Kudus, da kuma dukan kawo wuka da su ka yi wa ‘yan sahayoniya masu kwacen kasa, kuma azzalumai, sun taka wani mataki a fagen ayyana makomar wannan yakin baki daya, da kuma duniyar musulmi baki daya.

Yadda Amurka da ‘yan korenta suka nace wajen kare gwamnatin masu kwace kasa, ba komai ba ne,sai fakewa da guzuwa domin su hare siyasarsu ta amfani da ‘yan sahayoniyar domin shimfida ikonsu akan albarkatu da arzikin da yake a wanann yankin domin amfani da su a fadace-fadacen da suke yi a duniya. Abinda su ke son yi shi ne mayar da wanann haramtacciyar kasar zuwa cibiyar samar da makamashi a cikin wanann yankin da fitar da shi zuwa kasashen yammacin turai. Da kuma shigo da wasu kayayyakin masarufi da al’adun turai zuwa wannan yankin. Wannan shi ne zai bayar da tabbacin cigaba da zaman wannan ta kwace. Da kuma mayar da dukkanin kasashen da suke cikin yankin masu biyayya a gare ta.

Halayyar zubar da jinin ‘yan gwagwarmaya  ta wawan shugaban wannan haramtacciyar kasa, manufarsa ita cimma wannan manufa.

A dalilin haka, duk wanda yake raunan wannan  haramtacciyar kasa,ko kuma wata jama’a mai alaka da ita, to yana yi wa wannan yankin hidima ne. Yana ma yi wa dukkanin bil’adama hidima ne.

 Shakka babu wannan tunanin na ‘yan sahayoniya da Amurkawa, ba komai ba ne sai mafarkin tsaye. Wannan haramtacciyar kasar, tamkar mummunar bishiya ce, wacce aka tunbuke ta daga kan kasa, kuma zancen Allah madaukakin sarki ya dace da ita: “ Ba za da  wata matabbata.” Surat Ibrahim: 26

Wannan mummunar haramtacciyar kasa ba ta da jijiyoyi, kuma tabogi ce, mai raurawa. Ta hanyar taikamon da Amurka take ba ta ne, take rayuwa, kuma da iznin Allah ba za ta dawwama ba. Dalili akan haka kuwa shi ne, an ba ta biliyoyin daloli a kan fada da Gaza da Lebanin a cikin shekara daya, ana kuma ba ta nau’oin taimako daga Amukra da sauran kasashen yamma, amma kuma ta sha kashi a hannun adadin masu jihadi saboda  Allah da ba su wuce dubbai ba, wadanda kuma aka killace su, akan hana su duk wani taimako daga waje. Nasarar da ita ce kawai suka samu ita ce rusa gidaje da makarantu da asibitoci da duk inda fararen hula suke taruwa.

Yanzu an wayi gari, su kansu ‘yan dabar ‘yan sahayoniya sun yarda da cewa ba su cimma wata nasara ba, akan Hamas da Hizbullah.

Ya kuma mutanenmu ‘yan gwagwarmaya a Lebanon da Falasinu! Ya kuma masu fafatawa ma’abota jarunta! Yak u al’umma ma’abociyar hakuri da amana! Shahadar da kuke yi, da jinin da ake zubarwa,  ba sa  girgiza azamarku, suna kara muku tsayin daka ne.

A nan  jamhuriyar msuulunci ta Iran a cikin watanni uku a shekarar 1981, an yi wa fitattun mutanenmu kisan gilla, daga cikinsu da akwai irin su Sayyid Muhammad Beheshti, da shugaban kasa, Raja’i, da Fira minist  Bahonar. An kuma kashe malamai irin su Ayatullah Madani, da Qudduai, da Hashimi Nejad, da makamantansu. Kowane daya daga cikinsu ginshiki ne a jiyin musulunci, a cikin yankisa da kuma kasa baki daya. Rashinsu da aka yi bai zama abu mai sauki ba,amma duk tafiyar juyin juya hali ba ta tsaya ba. Ba ta ja da baya ba, ta ma kara habaka ne.

To a wannan lokacin ma gwagwarmaya ba za ta ja da baya ba a cikin wannan yankin saboda shahdar da mazajenta su ka yi. Gwgawarmaya za ta yi nasara. Gwgawarmayar mutanen Gaza ta dugunzuma tunanin mutanen duniya, ta kuma daukaka musulunci. Hakikanin gaskiya a Gaza an rika kai wa musulunci ne kai tsaye hari, da dukkanin munanan hanyoyi da sharri. Kuma babu wnai dan’adam da baya yin jinjina ga tsayin Dakar mutanen Gaza, ya kuma la’anaci mai adawa da ita,masha jini.

An cika shekara daya daga farmakin”Guguwar Aqsa’ a Gaza da kuma Lebanon, amma har yanzu abinda yake damu wannan haramtacciyar kasar shi ne kar samuwarta ta zo karshe. Wannan shi ne tunanin da yake damun wannan haramtacciyar kasa tun farkon kirkrirarta. Wannan yana nufin cea jihadin mutanen Flasdinu da Lebanon ya mayar da ‘yan sahayoniya shekaru 70 a baya.

Babban abinda yake kawo yake-yake da rashin tsaro a cikin wannan yankin shi ne kafa tsarin sahayonanci da aka yi a cikinsa, da kuma shigowar wasu kasashe da suke riya cewa suna son tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin yankin. Babbar matsala a cikin wanann yankin ita ce tsoma bakin da bakin haure suke yi a cikinsa. Kasashen wannan yankin za su iya shimfida tsaro da zaman lafiya a cikinsa. Kuma cimma wannan babbar manufa, da kuma tseratar da al’ummu yana da bukatuwa da yin kwazo daga al’ummun yankin da kuma gwamnatocinsa.

Allah yana tare da masu tafiya akan wannan tafarkin. ( Allah yana da karfin dai ba su nasara.) suratu Haj;39.

Amincin Allah ya tabbata ga jagora shahidi, da kuma gwarzo shahid Haniyyah. Da kuma kwamanda abin alfahari janar Kassim Sulaimani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments