Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gargadi yahudawan sahayoniyya kan kaddamar da duk wani harin wuce gona da iri kan kasar Iran, yana mai cewa: Martanin da Iran za ta mayar kan duk wani hari da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila za ta kaddamar zai zame mai tsanani da gauni, kuma ga fili ga mai doki.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya fada a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Damascus na kasar Siriya cewa: Akwai muhimman batutuwa guda biyu na gaggawa a kan ajandanmu, wadanda suka hada da tunkarar matsalolin ‘yan gudun hijiran kasar Lebanon da suka rasa matsugunansu, da samar da Shirin tsagaita wuta a Gaza da Lebanon.
Araqchi ya ci gaba da cewa: Sun gudanar da tattaunawa mai ma’ana, kuma zasu ci gaba kan batun gabatar da agajin jin kai ga ‘yan gudun hijiran kasar Labanon da tura da kasar Siriya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Martanin Iran kan duk wani harin yahudawan sahayoniyya a fili yake, domin kowane mataki yana da gwargwado irin martaninsa, kuma wannan shi ne abin da Iran ta tabbatar a baya.