Venezuela Ta Bukaci A Kafa Kawancen Kasa Da Kasa Don Kawo Karshen Kissan Kiyashin Da HKI Take Yi A Gaza

Ministan harkokin wajen kasar Venezuela Yvan Gil ya bukaci kasashen duniya musamman Iran da sauran kasshen larabawa su hada kai don kafa kawance wacce zata

Ministan harkokin wajen kasar Venezuela Yvan Gil ya bukaci kasashen duniya musamman Iran da sauran kasshen larabawa su hada kai don kafa kawance wacce zata kawo karshen kissan kiyashin da gwamnatin HKI ta ke yi a Gaza kimani shekara guda da ta gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadara haka ne a jiya Jimma’a a lokacinda ya tara jakadun kasashen Iran, Palasdinu, Lebanon, Syria, Kuwait, Algeria, Masar, Saudi Arabia, Iraq, Qatar da kuma Sudan a birnin Caracas babban birnin kasar.

An gudanar da taron jakadun wadan nan kasashe ne tare da bukatar shugaban kasar ta Venezuela Nicolas Madoro. Gil ya kara da cewa shugaba Madoro yana bukatar a kafa kawancen kasashen duniya don tabbatar da cewa an kawo karshen sabuwar gwamnatin ‘NAZI” ta Natanyahu. Ya kuma kara da cewa tun bayan gwamnatin Adof Hitaler a cikin karnin da ya gabata ba’a sake samun wata gwamnati mai kama da ita ba kamar gwamnatin Natanyahu.

Ministan ya kara da cewa abinda yafi haka muni shi ne goyon bayan da gwamnatin kasar Amurka take bawa Natanyahu 100% . Sannan da yin shirun da mafi yawan kasashen Turai suka yi kan wannan al-amarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments