Dokar Ta-Baci A Dukkanin Ofisoshin jakadancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Duniya

Tashar Talabijin ta 12 ta haramtacciyar Kasar Isra’ila ta sanar da ayyana dokar ta baci a dukkanin ofisoshin jakadancinta da ke kasashen biyo bayan harin

Tashar Talabijin ta 12 ta haramtacciyar Kasar Isra’ila ta sanar da ayyana dokar ta baci a dukkanin ofisoshin jakadancinta da ke kasashen biyo bayan harin birnin Beirut a wannan Juma’a.

Tashar  NBC News ta kasar Amurka ta bayar da rahoton cewa: hukumomin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun ce suna hasashen harin ramuwar gayya a kansu da kuma kaddarorinsu  bayan harin da aka kai a hedikwatar kungiyar ta Hizbullah a wannan Juma’a.

A yammacin jiya Juma’a ne jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a yankunan da ke yankin ​​Harik da ke kudancin birnin Beirut. Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin cewa makasudin wadannan hare-haren shi ne kisan babbar kungiyar Hizbullah da kuma wasu kwamandojin kungiyar.

Tashar Talabijin ta 12 ta gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta sanar da haka a cikin rahotannin da ta bayar bayan kai harin.

Kamfanin dillancin labaran Sama News cewa, ya bayar da rahoton cewa, sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a yankunan kudancin birnin Beirut har sau 10 a ranar Juma’a.

Kakakin rundunar yahudawan sahyoniya ya kuma yi ikirarin cewa, wannan gwamnatin ta yi ruwan bama-bamai ne kan hedkwatar kungiyar Hizbullah da ke karkashin gine-gine a tsakiyar yankunan kudancin birnin Beirut.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments