Hizbullah Ta Kasar Lebanon Tana Ci Gaba Da Kai Hare Hare Da Makamai Masu Linzami A Kan Wurare Da Dama A HKI

Labaran da suke fitowa daga HKI sun bayyana cewa ana jin karar jiniyar gargadi a wurare da dama a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye,

Labaran da suke fitowa daga HKI sun bayyana cewa ana jin karar jiniyar gargadi a wurare da dama a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye, daga cikin har da wasu garuruwa a yankin yamma da Kogin Jordan, Galilee na tsakiya da galilee na sama.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar na cewa garuruwan da abin ya shafa sun hada da Haifa da Came, da wasu wurare fiye da 100 a safiyar yau Asabar.

Larabarin ya kara da cewa, majiyar sojojin HKI sun bayyana cewa, wuraren da makaman kungiyar suke faduwa sun hada da  Rumana, Hanaton, Uzeir, Moran, Bir al-Maksur, Rumat al-Heib, Dmeide, Kfar Manda, Beit Rimon, Ras al-Ein, Shfaram.

Har’ila yau makamai masu linzami na kungiyar Hizbullah sun fada kan kamfanoni da masana’antu da dama daga ciki har da masana’antu a Pelekh, Majd al-Krum, Afek, Achihud, Yarka, Karmiel, Julis da kuma Acco.

Har’ila yau makaman sun fada kan Tzurit Gilon, Bar-Lev, Tuval, da kuma  Yasur.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments