Kwamnadan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce Hizbullah Ce Za Ta Yi Nasara

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ta bayyana cewa: Kungiyar Hizbullah ce za ta yi nasara tare da dakile shirin makiya yahudawan

Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ta bayyana cewa: Kungiyar Hizbullah ce za ta yi nasara tare da dakile shirin makiya yahudawan sahayoniyya

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Da a ce kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma dukkan bangarorin da ke da alaka da shaidanun duniya ‘yan sahayoniyya za su hadu wuri guda, da yardan Allah ba za su taba samun nasara kan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Manjo Janar Salami ya bayyana cewa: Da yardan Allah Madaukaki kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ce za ta samu nasara a wannan karo kamar yadda ta samu a baya tare da dakile shirin makiya, a daidai lokacin da kungiyar Hizbullah ke fadada kai hare-hare da makamai masu linzami kan wurare masu muhimmanci da yahudawan sahayoniyya suka mamaye.

Salami ya ce: Suna da tabbacin cewa; Lallai al’ummar Falasdinu nan ba da dadewa ba za su samu gagarumar nasara. Ya kara da cewa: Kungiyar Hizbullah jaruma ce a kasar Lebanon mai dauke da tutar daukaka da jihadi da kuma karfi, tana yakar makiya a wuraren karo da juna da kuma samar da wata sabuwar nasara mai daraja a kowace rana, a wannan fage kamar yadda ya faru a baya, za ta yi nasara da alfahari kuma zata kara ruguza duk wani gurin makiya da cusa musu takaici.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments