Qalibof: Babban Matsalar Kasashen Yakin Asiya Ta Kudu Itace HKI

Kakakin majalisar dokoki ko majalisar shoora Islami na JMI Mohammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa babban matsalar kasashen yankin Asiya ta kudu ita ce samuwar

Kakakin majalisar dokoki ko majalisar shoora Islami na JMI Mohammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa babban matsalar kasashen yankin Asiya ta kudu ita ce samuwar HKI  a yankin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Qolibof yana fadar haka a taron kwamandojojin sojojin JMI karo na 36TH kuma a cikin ranakun makon yaki mai tsarki, ko yakin kare kasa na tsawon shekaru 8 wanda JMI ta yi da gwamnatin Iraki na lokacin.

Qalibof  yana kara da cewa Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya bayyana a farko nasarar juyin juya halin musulunci a kasar kan cewa HKI cutar kance ce a gabas ta tsakiya kuma dole ne a shafeta daga samuwa.

Kuma ya kara da cewa hanyar kwato birnin Qudus zai ta Karbala ne, wato daga kasar Iraki. Kakakin majalisar dokokin kasar Iran ya nakalto sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken yana fada a farko farkon yakin tufanul akasa kan cewa, idan da babo Isra’ula to ya zama dole su samar da ita.

Wannan ya tabbatar da zancen Imam na cewa kasashen yamma sun samar da HKI a tsakanin kasashen musulmi ne don shagaltar da su. Sannan sun yi amfani da kungiyar ISIS har suka zo kusa da kan iyakar kasar Iran amma Shaheed  Kasin Sulaimani da tawagarsa sun rusa su.

Yace har yanzon sojojin kasar Iran a shirye suke su fuskaci duk wata barazana ga kasar. Sannan zata ci gaba da tallafawa masu gwagwarmaya da HKI har zuwa karshenta a yankin. Wannan duk atare da tallafin da take samu da kasashen yamma da kuma kungiyar tsaro ta NATO.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments