Sudan: Tabarbarewar Harkokin Kiwon Lafiya A Darfur Yana Daukar Rayukan Mata Da Kananan Yara

Kungiyar Likitocin Sa-Kai ta ( Doctors Without Borders) ta bayyana cewa, mata da kananan yara suna mutuwa a yankin Darfur akan cutukan da za a

Kungiyar Likitocin Sa-Kai ta ( Doctors Without Borders) ta bayyana cewa, mata da kananan yara suna mutuwa a yankin Darfur akan cutukan da za a iya magance su, saboda rashin magani da kayan aiki.

Rahoton da kungiyar ta fitar ya kunshi cewa; Daga watan Janairu na wannan shekara zuwa tsakiyar Ogusta, an sami mutuwar mata da kananan yara har sau 114.

Har ila yau, rahoton ya kuma ce, kaso 50% na wadanda su ka rasu, ya kasance ne a asibiti da kuma cibiyoyin kiwon lafiya a yankin Darfur, saboda a can ne ake da cibiyoyin kiwon lafiya mafi tabarbarewa a duniya.

A cikin watan Ogusta kadai an sami kananan yara 30,000 wadanda suke fama da tamowa.

A jiya Talata ne dai kungiyar ta “Doctors Without Borders” ta fitar da rahoton tana mai kara da cewa, abinda yake faruwa sakamako ne na             yakin da kasar ta tsunduma a cikinsa tun daga watan Aprilu na 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments