Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Kawo Karshen Yakin Zirin Gaza Na Falasdinu

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Dole ne a dakatar da hare-haren wuce gona da iri da ake kai wa kan Zirin Gaza na Falasdinu

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Dole ne a dakatar da hare-haren wuce gona da iri da ake kai wa kan Zirin Gaza na Falasdinu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Tilas ne a kawo karshen kai farmakin da haramtacciyar kasar Isra’ila take kai wa Gaza ba tare da bata lokaci ba, yana mai jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su yi kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta dindindin a Gaza.

A farkon jawabinsa a zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na saba’in da daya, shugaban kasar ya yi tabo juyayin tunawa da marigayi shugaban kasar Iran, shahidi Ibrahim Ra’isi, inda ya ce: A shekarar da ta gabata, shugaban shahidi Ra’isi ya yi magana da ku a daidai wannan wuri, amma a halin yanzu ya yi shahada a daidai lokacin da yake hidima ga al’ummar Iran.

Pezeshkian ya yi nuni da yadda aka gudanar da zabe a kasar Iran bayan rasuwar tsohon shugaban kasarta, Shahidi Ibrahim Ra’isi, da kuma yadda al’ummar kasar suka shiga zaben, inda ya ce: Al’ummar Iran sun zabi taken neman hadin kan kasa, inda hakan ya yi daidai da umarnin Allah a cikin Alkur’ani mai girma, domin dukkan ‘yan Adam daga asali guda suke.

Yana mai jaddada cewa: “Shi ne shugaban ƙasar da aka yi wa barazana, da yaƙe-yaƙe, da kuma mamaya sau da yawa a cikin tarihinta,” yana mai cewa: “Yana da burin kafa ginshiƙai masu ƙarfi don ƙasarsa ta shiga sabon zamani kuma ta taka rawa mai inganci sannan mai mai kima cikin tsarin sabuwar duniya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments