A Karo Na  Biyar An Yi Taro  A Tsakanin MDD, Tarayyar Turai Da Tarayyar Afirka

Taron ya mayar da hankali ne a tskanin bangarorin uku domin tattauna hanyoyin tabbatar da zaman lafiya, cigaba da raya yankin Sahel da kuma zirin

Taron ya mayar da hankali ne a tskanin bangarorin uku domin tattauna hanyoyin tabbatar da zaman lafiya, cigaba da raya yankin Sahel da kuma zirin Afirka.

An yi wannan taron ne dai a  jiya Lahadi a birnin Newyork a zauren MDD inda ake yin taron shekara-shekara domin tattauna matsalolin da su ka ci dunun duniya.

Babban magatakardan MDD Antonio Gutteress, ya gana da shugaban tarayyar Afirka Musa Fakih, da kuma shugaban majalisar tarayyar Turai Charles Micheal, sai kuma babban jami’in wannan tarayyar mai kula da harkokin wajenta Joseph Boril.

Duka bangarorin uku sun cimma matsaya akan yin aiki tukuru a tsakanin bangarori mabanbanta.

Har ila yau bangarorin uku sun tattauna akan hanyoyin shimfida zaman lafiya da raya kasa a cikin yankin Sahel da zirin Afirka da kuma yankin tekun Victoria,tare da jaddada muhimmancin mayar da hankali akan bunkasa rayuwar mutanen yankin daga ciki har da Sudan da ake da mutane fiye da miliyan 25 da suke fuskantar matsaloli saboda yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments