Hizbullah Ta Kashe Sojojin HKI A Wani Hari Da Ta Kai A “Jalil-A’ala”

A yau Alhamis ne kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa ta kai hari da makamai masu linzami akan sansanin soja na HKI

A yau Alhamis ne kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa ta kai hari da makamai masu linzami akan sansanin soja na HKI dake yankin Jalil-A’ala, tare da kashe da kuma jikkata sojojin mamaya.

Sanarwar ta Hizbullah ta kara da cewa, ta kai wannan harin ne a matsayin taya Falasdinawa fada da kuma goyon bayan gwgawarmayar al’ummar Falasdinu.

Tashar talbijin din ‘almayadin” ta ambaci cewa; Hizbullah ta kai wani harin akan motar HKI dake yankin “Tal-Hawi” a kusa da Kiryat-shimona” ta hanyar amfani da makami mai linzami dake fasa motoci masu silke.

 A gefe daya, sojojin mamayar HKI sun harba makaman “Pusporus’ da aka haramta amfani da su a duniya, a kudancin Lebanon, haka nan kuma an ji karar saukar jirgi mai saukar angulu wanda ya sauka domin dibar wadanda su ka jikkata.

Kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa harin na Hizbullah ya yi sanadin kashe sojan mamaya da kuma jikkata wasu biyar a kusa da matsugunin ‘yan share wuri zauna na “Har Dof”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments